FA'IDODIN GANYAN MANGWARO

[ Go to bottom  |  Go to latest post  |  Subscribe to this topic  |  Latest posts first ]


admin
Admin

44, male

Posts: 3

FA'IDODIN GANYAN MANGWARO

from admin on 11/10/2017 05:00 AM

*FA'IDODIN GANYEN MANGWARO,MUSAMMAN WAJEN MAGANIN CIWON SUGA DA HAWAN JINI DA SAURANSU*: .....Balarabe Shehu Illelah, kasar Sin (China)..... Ko kun san cewa masana ilimin kimiyyar magunguna, na kasar Sin da India, sun tabbatar da cewar daya daga cikin manyan magungunan warkar da ciwon suga (diabetes) shine *Ganyen Mangwaro*? *Ganyen Mangwaro* na dauke da sinadarai masu yawan gaske da ke amfana wa jikin Dan’adam, amma kash, mutane da dama basu san hakan ba ! Yadda ake amfani da shi a matsayin *Maganin cutar ciwon Suga* ( Diabetes) (1) A tsinko ganyan Mangwaro,masu kyau. A wanke su sosai (2) A sanya ruwa a murhu, a tafasashi, har na tsawon minti biyar ba tare da ganyen ba. (3) Sai a zuba ganyen a cikin ruwan zafin da ke kan murhu,tare da OLIVE Oil (wato Man Zaitun). A barshi yayi ta tafasa, har na tsawon mintuna biyar zuwa goma. (4) Sai a sauke shi a tace. (5) Sai a sanya shi cikin kwano ko gilashi mai kyau, a barshi ya kwana (6) Sai a sha wannan ruwan da sassafe bayan an tashi daga barci, kafin ka ci komai. Wannan maganin, yana kawar da abubuwa (marasa kyau masu guba) daga jikin mutum, kuma yana rage yawan suga da ke cikin jini. Haka kuma yana saukar da hawan jini sosai. *ASTHMA,TARI, KO MATSALAR NUMFASHI* yakan sa a samu numfashi mai kyau,kuma cikin sauki,da yardar Allah. *YAWAN FARGABA, ZAMAN DAR-DAR KO RASHIN NUTSUWA* (restlessness): Idan aka zuba cokali biyu zuwa uku, a cikin ruwan wanka, sannan ayi wanka dashi. Yana sanya aji jiki garau, kuma aji hankali ya kwanta,da yardar Allah. *DUTSEN DAKE ZAMA CIKIN HANTA,MADATA KO KODA* (wato *kidney stone*). Mai wannan ciwon, zai busar da ganyen Mangwaro (a inuwa), sannan ya daka shi. A zuba garin a cikin kofi/glass ko kwano, a barshi ya kwana. A rinka sha kullum da safe. Wannan yana narkar da dutsen dake jikin koda sosai,da yardar Allah (swt). *CIWON TARI,GUSHEWAR MURYA KO ASTHMA* A dafa ganyen Mangwaro, a sanya masa Zuma (kadan). Yana taimakawa kwarai da gaske cikin sauri. *CIWON ATINI,KO KASHIN JINI* Sai a shanya ganyen a inuwa a busar dashi a kuma mayar dashi gari, a rinka sha sau uku a rana . Yana tsayar da cutar atini. *CIWON KUNNE* Idan aka tatse ruwan ganyen Mangwaro aka dan dafa shi, sai a rinka digawa a cikin kunnen. Wannan yana *maganin ciwon kunne*. *KUNAR WUTA* Sai a kona ganyen Mangwaro har ya zama toka. Sai kuma a rinka barbadawa a wurin da aka kone. Yana warkar da kunar cikin sauri. Zai kuma bushe da gaggawa In Sha-Allahu. *YAWAN SHAQUWA DA CIWON MAKOGORO* Idan ana shakuwa ko zafin makogwaro,sai a kona ganyen Mangwaro a shaki hayakin. Yana *tsayar da shakuwan da ciwon makogwaro*. *CIWON CIKI* Idan ana yawan *Ciwon Ciki* sai a sanya ganyen Mangwaro a cikin ruwan dumi, a barshi ya kwana, sannan a sha da safe kafin aci komai. In an juri yin hakan yana warkar da *Ciwon Ciki* kowane iri ne,in Allah Ya yarda. *Shan ganyen mangwaro a kai a kai yana kuma kara inganta garkuwan jiki kuma yana maganin hana kumburin ciki*. Yana da kyau ka jurewa shan ganyen Mangwaro a duk safiya, domin ganin yadda suga dake cikin jikin ka, zai sauka cikin sauri in Allah (SWT) Ya yarda.

Reply

admin
Admin

44, male

Posts: 3

Re: FA'IDODIN GANYAN MANGWARO

from admin on 11/10/2017 05:04 AM

Allah ka sa mudace

Reply

« Back to forum