Shin suwane zasu zauna A inuwar Alarshi

[ Go to bottom  |  Go to latest post  |  Subscribe to this topic  |  Latest posts first ]


admin
Admin

44, male

Posts: 3

Shin suwane zasu zauna A inuwar Alarshi

from admin on 11/07/2017 01:59 PM

WADANDA ZASU ZAUNA KARKASHIN INUWAR AL'ARSHI : TAMBAYA TA 2395 ******************** Assalamu alaykum Allah ya kara muku lafiya ya baku ladan taimakonmu da kukeyi, pls inada question and it's kind of urgent Allah yasa ku samu damar amsa min. Dan Allah hadith guda 1 nake son ku fada min wanda aka irgo wanda zasu shiga karkashin al'arshin Allah ranar alkiyama (banda hadith din da yake cikin bughyatu kulli Muslim). Jazakumullah AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Shi wancan Mashahurin hadithin da kike fada, ina jin shine wanda Imamul Bukhariy da Muslim da Nisa'iy da Tirmidhiy da Imamu Malik suka ruwaitoshi ta hanyar Sayyiduna Abu Hurairah. To bayan Abu Hurairah din an ruwaito irinsa ta wajen Sahabbai da dama kamar : - Abu Sa'eed Alkhudriy. - Salmanul Farisiy. - Abud Darda'i. - Mu'az bn Jabal. - Al'irbaadh bn Sariyah. (Yardar Allah ta tabbata garesu baki daya). To bayan shi akwai wani hadisin Sahihi wanda aka ruwaito daga wani Sahabi mai suna Abul Yusri (ra) yace "Naji Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yana cewa : "DUK WANDA YA JINKIRTA MA WANDA YAKE CIKIN TSANANI KO KUMA YA SAUKE MASA (BASHIN DA AKE BINSA KENAN). TO ALLAH ZAI INUWANTAR DASHI ARANAR DA BABU WATA INUWA SAI TASA". Abdu bn Humayd da Imamu Ahmad sun ruwaitoshi acikin Musnadansu. Imamu Muslim ma ya kawo wani hadisin mai irin Ma'anarsa acikin wata Qissah. Haka ma Ibnu Maajah. Imamud Daramiy ya ruwaito wani hadisin SAHIHI acikin Musnadu nasa ta hanyar Abu Qataadah (ra) yace Naji Manzon Allah (saww) yana cewa : "DUK WANDA YA JINKIRTA MA WANDA YAKE BI BASHI, KO KUMA YA SHAFE MASA BASHIN, TO ZAI ZAMANTO ACIKIN INUWAR AL'ARSHI ARANAR ALQIYAMAH". Ga wani ma daga Sayyiduna Anas bn Malik (rta) daga Manzon Allah (saww) yana cewa : "MUTUM UKU SUNA CIKIN INUWAR AL'ARSHIN ALLAH ARANAR DA BABU WATA INUWA SAI DAI TASHI : - WANDA YA YAYE DAMUWAR WANI MAI DAMUWA DAGA AL'UMMATA. - WANDA YA RAYA SUNNAH TA. - DA KUMA WANDA YA YAWAITA SALATI AGARENI". Daylamiy ne ya ruwaitoshi. To ga guda uku nan domin Qarin fa'idah. Idan kuma ana buqatar wasu, aduba littafin Imamus Suyutiy mai suna "BUZUGUL HILAAL". WALLAHU A'ALAM. DAGA ZAUREN FIQHU (07-11-2017 18-0

Reply

« Back to forum